MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SAKO ZUWA GA MATAN AURE

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, awannan zamanin da muke ciki, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba zata ga wasu ‘yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkhairi agareki ki Qudurce acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI.

Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku. Kuma ki zama ko yaushe ashirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.

Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE… Ba zasu rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji, su kuwa basu samu ba… Dole suyi miki hassada.

Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa.. Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa.. Don haka kar ki gaya musu.

Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula dasu, ki kula da tsaftarsu. in ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula dasu kamar yadda zaki kula da ‘ya’yanki.

Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki. musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-10-02 — 8:52 am

5 Comments

Add a Comment
 1. shema'u salis dirimin iya

  Allah ya saka da alkhairi Allah ya bamu miji nagari

 2. Almuneer Suleiman Aliyu

  Allah ya saka maji da alheri

 3. Allah ya saka da alakairi naji dadin wannan shawara sosai dan Allah inason kucikaba daba iyayen mu mata shawara akan gwadayin abun duniya da suke daura yaransu mata akai nagode

 4. Ismail Usman Abubakar

  Munajin Dadin Shirye Shiryenku.

  1. MUMA GODIYA MUKE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme