MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MATSAYIN KUNYA A MUSULUNCI

KUNYA DUKKANSHI ALKHAIRI NE!

الحياء كله خير

Kunya Yana daga cikin abunda mutanen wannan zamani (da dama daga cikin mu) muka rasa, daga mazanmu har mata, alhali kuwa kunya wani kaso ne/yanki ne na imani

.
Annabi (sallallahu alayhi wa sallam) wata rana yazo wucewa (inji dan-umar) saiya tarar da wani mutum cikin mutanen madinah yana yiwa dan-uwanshi wa‘azi akan kunya (ma‘ana kunyanshi yayi yawa/ka rage kunya dss) sai annabi yace dashi,
دعه فإن الحياء من اﻹيمان
Ma‘ana Annabi yace ma wannan mutum ka kyale shi, ai ita kunya tana daga cikin imani.

WANNAN MUMMUNAN DABI’A TA ZAMA RUWAN DARE MUSANMAN A DA DAMA DAGA CIKIN MAKARANTU NA GABA DA SECONDARY
Ta yadda zakaga mutanenmu tamkar bamu ba, an dauki rigar mutunci/kunya an aje a gefe, wasun da sunan yanci ya samu wasun da sunan wayewa wasun makamancin haka…

alhali kuwa annabi cewa yayi
A wani hadisin da kunya da imani dan-juma ne da dan-jummai (ma‘ana a hade suke da juna) muddin aka rasa daya to dayan baya zama, tafiya yakeyi
Muddin ka rasa kunya toka tun-tubi imaninka.

.
Wani hadisin annabi yace shi imani yana da rassa day-day har guda 70+ da doriya, mafi girma cikinsu shine fadin/furta kalman shahada (LA‘ILAHA ILLALLAH….)
Mafi qanqanta kuwa shine mutum ya kawar da abu me cutarwa daga kan hanya.
Sai annabi yace
والحياء شعبة من اﻹيمان
Ma‘ana ita kuma kunya wani sashi/kaso ne na imani.

SAIDAI KASH….

.
Mutane da yawa a wannan zamani da dama sun dauki wannan kaso na imani ba‘a bakin komai ba
Sun dauki kunya=gidadanci
Sun dauki rashin kunya=ado
Sun dauki zubda mutunci=wayewa

Mata kuwa
Sun dauki shigan tsiraici=cinyewa
Sun dauki shigan kamala=duhun kai/rashin wayewa
Sun dauki al-adun kafirai=zamananci

mutanenmu Sun dauki shaye-shaye da sauran duk wani yakan rashin kunya ya zama tamkar aikin lada ko kuma ba komaiba!

ILLOLIN DA RASHIN KUNYA YAKE JAWO WA
1-tawaya na imani
2-gushewar kamala
3-kwaranyewar kwarjini
4-zubewar mutunci
5-bayyanar jahilcin meshi a fili
6-da sauransu
.
AMMA ABUN TAKAICI
Da dama suna ADO da irin wannan hali/shiga/dabi‘u/­­halayya na rashin kunya kuma agaban iyayensu ba tare da jin ko dar-dar ba.
.
Wani ubanma inka tabashi akan ya kula da halayyan ya-yansa dabi‘unsu da halayyansu, al-adunsu da dibinsu(musanman mata) sai yace dakai, ka barsu zamani ne, ai duk abunda zasuyi bazasu kaimu ba! (wa‘iyazu biLla)

Yanzu har takaiga babu wani gari ko kauye da bazaka samu WIXY ba, (irin masu sabule wando dinnan da sunan zamananci)

To iyaye ku sani annabi yace
الحياء لا يأتي إلا بخير
awata ruwaya yace
الحياء كله خير
Ma‘ana ITA KUNYA BATA ZUWA DA KOMAI FACE ALKHAIRI
Wani wajen yace KUNYA DUKKANTA AL-KHAIRI NE
.
MA‘ANAR WANNAN HADISI SHINE
Rashin kunya kuma bata zuwa da komai face sharri
Sannan kuma rashin kunya dukkanta sharri ce

Yan-uwa mu kula da halayyan iyalanmu domin kiwo aka bamu na mu lura da tarbiyyansu,halayyan­­,dabi‘unsu,mu‘amala­n­su da mutane,

Domin shakka babu za‘a tambayemu.
.
Allah ubangiji ka gyara mana halayyan qannenmu,yayan-mu da sauran musulmai baki daya

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-10-23 — 7:44 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme