MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MAI KESA WASU IYAYE HANA ‘YA’YANSU SOYAYYA DA WASU SAMARI

Kamar yadda muka saba a kowane mako, dandalin voa yana kawo maku ra’ayoyi da muhawara akan abubuwa da dama da suka shafi matasa, zamantakewa da kuma harkokin soyayya.

A wannan makon, mun sami zantawa da wasu samari ne domin jin ra’ayoyin su musamman akan dalilna da ke sa wasu iyaye hana ‘ya’yan su soyayya da wasu samari, koda shike dalilan nada dama kamar yadda yawanci suka bayyana amma yawanci sun fi bada fifiko akan tarbiyya.
Idan matashi bai da tarbiyar kwarai kokuma ya fito daga gidan da ake gani a matsayin maras mutunci, lallai zai yi wuya samarin gidan su sami aure da sauki kamar yadda wasu ke samu.

Haka kuma, rashin ilimin boko da na addini yakan sa wasu iyaye su kyamaci bada diyan su aure a cewar wasu daga cikin matasan.

Daga Dandalinvoa.com

Updated: 2017-12-22 — 6:56 pm
 1. ha ghhfd

 2. aliyu shehu abubakar

  Rashin bin Qaidan neman aure, don kowa nason auradda yansa ko Dansa gidan Tarbiya.wasu iyayen kuma kwadayin abin Hanune.

 3. Ba wani abu makasudin duk irin matsalolin da muke fuskanta ayau face kaucewa doran tarbiyyar addini da kuma bin sunnar manxon allah (saw)

 4. Nasiru Rabi'u Gumel

  Allah yasa mudace amin

 5. hmmmm gaskiya soyayya Dadi fa Yan uwana

 6. Gaskiya lamarin tarbiyya dakuma ilimi shine abin da yafi yasiri a bangaren Neman aure ga masu tunani.

 7. Aminu yakubu kazaure

  To Allah yasa mu dace

 8. Allah yasa mu dace amin

 9. toh,Allah ganan da iyayen maza kuma Wanda beda abinyi Allah bashi

 10. Zamani ne ya change ya allah shikyau tah

 11. wasu iyayen kana fara neman yarsu zasu fara tambaya mikake dashi ko me iyanka sukedashi.

 12. to naji kowa ya tofa albarkacin bakinshi, amma nidai da’abani budurwa, gara anbani buhun goruba.

 13. Bello Abdullahi Dole

  Allah ya sawake amen

 14. Rabilu Yusha,u Gama

  Ba talaka ne shi kansa talauci abin gudu ne

 15. Wasu kuma iyayensu basasan talaka

 16. Saboda basuda tarbiya mai keu kuma wasu mazan bana korai bane

 17. gaskiya tarbiya da rashin aikin yi suna kawo a hana mutum aure Dan wasu iyayen ba ruwansu da dukiyarka

 18. Alhassan Sani Kura

  Gaskiya rahin tarbiya shine abu na farko sai kuma zaman banza shima yana daya daga cikin dalili da ake hana mutum aure

 19. Haka,kowane tsuntsu kukan gidansu yakeyi,wasu iyayen basa damuwa da rashin ilmin manemin ‘yarsu da zaran an fuskanci yanada maganin farin jini wato naira mai jin yare iri iri saisu bashi ‘yarsu,wasu iyayen kuwa ba ruwansu da ruwan kud’inka indai har zaka rik’e musu ‘yarsu da mutunci ba tare da sun dubi tulin dukiyar da kake da itaba sai kazama angon ‘yarsu,shidai mutunci hausawa sunce yafi kud’i kuma haka zalika shi mutunci madarane idan ya zube baya d’ebuwa,ku huta lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme