MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MAHIMMANCIN WANKAN MAGARYA WURIN KARYA ASIRI

wankan magarya

Wankan magarya nada matukar mahimmanci musamman yadda Muke cikin wani zamani wanda Imani yayi karanci ganin irin yadda asiri ya yawaita, har an kai ga makusanta ma suna wa juna domin kuwa uwa nayi ma danta ‘da yayi uwa ko mahaifi, mata tayi wa miji haka zalika miji ma yayi wa mata, ko kuma wajen aiki ko sana’a  yanzu wanda baka taba tsammani ba sai yayi maka asiri.

Akwai adduo’I  da dama da sunnah ta koyar da kuma mataikai irin kwanciya da Alwala da akeyi domin kariya daga tsafi ko mugun baki. Idan asirin ya riga ya kama mutun (domin shi asiri gaskiya ne  idan anyi yana ci shiyasa aka hana yin kuma aka tsine wa maiyin kuma aka ki yarda ayi, kamar bayanin da Malam Daurawa yayi a TAMBAYA MABUDIN ILIMI).

Idan anyi asirin ya kama mutun ya za’ayi a warware shi ba tare da anje wajen boka ba?

KARANTA KAJI: RIBAR YA MACE A GIDAN AURENTA

ABUBUWAN 6 DA YA KAMATA KAYI

  • Za’a samu ruwa mai kyau bokiti daya
  • Sai danyen ganyen magarya kwara bakwai
  • Sai a dandaka ganyen magaryan a zuba a ruwan a girgiza
  • Sai a karanta karanta Bakara daga farko har karshe (wani zai iya karantawa wani)
  • Sai a karanta Qula’uzzai (sautin karatun na shiga cikin ruwan)
  • Ruwan ne zaarika amfani das hi ana wanka ana sha tsawon kwana bakwai (Ba’ayi a ban daki)

In Allah yaso ya yarda idan asiri ne ko mugun baki ne idan aka samu kwana bakwai ya karye, sannan yana da kyau ka rike Azkar domin Kariya.

Anso ka rika yin wankan magaryan koda baka zaton za’a maka asiri.

Idan kaji dadin wannan bayanin zanso kayi comment a kasa da raayin ka sannan kayi sharing domin yan uwa su amfana.

https://instagram.com/mujallarmu

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme