MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ku karanta ZA’A SAMU MACE ME BIYAYYA KWATANKWACIN HAKA?

Wata Rana sayyaduna Aliyu R.t.a ya dawo daga wajen yaki ya gaji sai yake baiwa sayyada Fatima Labarin Abubuwan da suka faru a wajen wannan yakin saitace to kaga gashi ka gaji bari na kaima Ruwa kayi wanka bayan ta kaimai Ruwa yayi wanka yaci Abunci sai ya kwanta ya tada kai A jikin hannun sayyada Fatima A.s ita kuma tana shafa gashin kansa har bacci ya kwasheshi ita kuma ta fara gyangyadi saiga Annabi Muhammadu s.a.w yazo gidan su ya kawo musu gurasa, sai yayi Sallama Ita kuma nana fatima ga sayyaduna Aliyu R.t.a yana bacci a jikin hannunta kuma tasan daga yaki ya dawo ya gaji bataso ta tasheshi ga kuma mahaifinta a bakin kofa yana sallama saita dauki takobin yakin mijinta da take kusa da ita ta yanke hannun da sayyaduna Aliyu ya tada kai dashi sai Allah ya tsaida jinin ya hanashi zuba kasa, ta tashi ta tafi wajen Annabi s.a.w tana bude kofa Annabi s.a.w yaganta a wannan hali hankalinsa ya tashi yace meyake faruwa naganki da hannu daya Fatima A.s tace ya Abbana kaine ka umar ceni inyiwa mujina biyayya yaje yaki ya dawo ya kwanta a jikin hannuna yana bacci gashi kuma kayi sallama dolene inzo in Amsa kiranka sbd banaso in tadashi daga baci shiyasa nai haka tana gama magana Mala’ika jibrilu yazo wajen yace Ya Rasulillah s.a.w Allah yana gaida kai yana gaida fatima A.s kuma yace a gayama ya baiwa fatima A.s matsayin saddiqa, tundaga farkon duniya har gashenta babu wata mace mai matsayin saddiqa sai Nana fatima A.s A maza kuma Shine Abubakar saddiq R.t.a kuma Allah yace a gayama kaine shugaban kowa A cikin Mata kuma fatimace shugabar kowa a cikin samari kuma ‘yayanta su Alhasan da usaini sune shugabannin samarin gidan Aljanna nan dai mala’ika jibrilu yaita gaya musu Albishir iri iri daga Allah kuma Manzon Allah s.aw ya maida mata hannunta ya koma dai dai yana daga cikin matsayin saddiqa matsayine da babu wani matsayi a gabansa sai Matsayin Annabta sayyaduna Aliyu kuwa Annabi s.a.w yace duk wanda nake shugabansa to Aliyuma shugabansa ne Allah ka karamana kaunar su Ameen

(Visited 3 times, 1 visits today)
Updated: 2017-08-11 — 11:49 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme