MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI:ANATSE

                 KARANTA ANATSE.

*MISALI*


Bayan na dauki
wani lokaci mai
tsayi ina kwance
ina bacci sai naji
matata tana ta
tashina daga bacci,
babban abinda ya
bani mamaki shine
yadda na farka
kuma nakemata
magana cewa

ME KIKE BUKATA?

Amma ita kwata
kwata batajin
maganar da
nakemata, amma
ahaka tajuya ta
fita, bayan kamar
minti 30 sai ta
dawo takara
tashina na farka
nacemata

ME KIKEBUKATA?

Amma ina batasanma
inayiba. Kawai sai
naga ta fita waje
afirgice tana kiran
‘yan-Uwana. sai
naga ‘yan-Uwana
sunkira likita yazo
gurina yana gwada
jikina, sai nacema
likitan
ME KAKE BUKATA?

Amma wani abin mamaki
sai naga likitan
bayajin maganar
da nakeyi, sai naji
likita yana gayama
‘yan-Uwana cewa
na” mutu”. Sai suka
firgita sukai tayin
koke-koke duk
dacewa
banmutuba, ni dai
bansan dalilin da
yasa basajin
maganataba, wannan
abu yayi matukan
ban mamaki
musamman da naji
‘yan-Uwana
sunacewa
“agaggauta ayi
jana’izata”, sai naga
sun daukeni
sunkaini dakin da
nake ajiye
motocina, ga shidai
inayimusu magana
amma kwata
kwata basajin
maganar da nakeyi,
sai suka ciremini
tufafina sannan
suka yimini wanka
suka samini
likkafani kuma
suka daukeni suka
kaini masallaci don
ayimini sallah. Na
samu liman na
gayamasa cewa
da raina ban
mutuba, amma sai
naga liman yaki ya
kulani inaji ina gani
sukaimin sallah,
bayan sungama
yimin sallah sai
suka daukeni suka
nufi makabarta
dani inaji ina gani
suka rika kokarin
binneni, bayan
sun sa ni acikin
kabari sai naga
wani daga cikin
‘yan-Uwana na
kusa wai har dashi
ake kokarin
binneni, sai
nacemasa

NIFA BAN MUTUBA

Dan haka karda ku
binneni, amma sai
naga ko kulani
baiyiba kamar
baisan inayimasa
maganaba, bayan
sungama zubamini
kasa sai na tuna da
Hadisin MANZON ALLAH (S.A.W)
ya ce “lallai mamaci
yanajin takun
takalman mutane
idan suka juya
zasu fita daga
maqabarta”, sai
nima narika jin
takun takalmansu
alokacinda suka
juya suka barni
acikin
kabari, wannan
shine abinda ya
tabbatar mini
cewa

AYANZU INA CIKIN WANI GURIMAI TSANANIN DUHU.

Bayan haka
sai wasu mazaje 2
masu firgitar da
jama’a sukazo
guna, 1 daga
cikinsu ya tsaya
akusa da kafafuna
1kuma ya tsaya
akusa da kaina
sannan aka
tambayeni

WAYEUBANGIJINKA?

Saina fara tunani
waye Ubngijina?
alhali nasan
Ubangijina dan
haka narika
mamakin yadda
akayi na manta,
haka da aka
tambayeni

WAYE ANNABINKA?

Nan fa na fara
tunani

ANNABINA! ANNABINA!! ANNABINA!!!

Sannan aka
tambayeni miye
ADDININKA? nanfa
nashiga tunani
addinina addinina
ga shidai nasan
amsoshin amma
abun mamaki shine
yadda na
manta, babu wani
abu da yake
fadomini arai bancin
matata da
shagona da ‘yan-Uwana da motata,
har saida naga
ansa wani katon
kulki andakeni
dashi duka mai
tsanani, nanfa na
saki baki na
kwarara ihu!

IHUN DA YA TAYAR DA
DUKKANNIN MUTANEN
GIDANMU.

Da sukeyin bacci, sai
matata ta kira
sunana sannan
tace:
MEYASA KAKEYIN IHU DA KA’RA IRIN HAKA?

Awannan lokacin
ne na gane cewa
mafarki nayi, nanfa
na tsaya inata
haki kawai sai naji
ankira sallar
asubah sai ya
zamana cewa
wannan mafarki
da nayi shine
sanadiyyar
shiriyata, tundaga
wannan ranar
narika dagewa
wajen yima ALLAH
(S.W.T) biyayya.

WANNAN KENAN gaskiya ‘yan-Uuwa Musulmai
muji tsoron ALLAH, domin watarana wannan labari zai faru akankowa wannan tunatarwace,
muna rokon ALLAH yabamu ikon amsa tanbayoyin
kabari.
YA ALLAH KADAUKI RANMU MUNA MUMINAI

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-09 — 3:29 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme