MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: SIFFA GOMA NA MATAR DA BA’A IYA MANTAWA DA ITA HAR ABADA

Mace Mai Siffofi  Goma  Itace  Kowane  Namiji  Ke Burin  Aura.

    

1, MATAR DA TA YARDA ITA MACE CE, DON HAKA TA TANADI DUK ABINDA AKE BUKATA A WAJAN MACE.

2, MACE MAI HIKMA, DA AZANCI, WACCE TA KARANTA MIJINTA DA KYAU, KUMA TAKE  KAUCEWA DUK ABINDA ZAI KAWO KARO TSAKANIN SU,

3, MACE MAI TAUSHIN HALI, DA NUTSUWA, WACCE MIJI YAKE JIN NUTSUWA, IDAN YANA TARE DA ITA.

4, MACE DA KUDI BAI DAMETABA, ITA MIJINTA KAWAI TAKE SO, KO DA AKWAI, KO BABU.

5,   MACE MAI HAKURI DA JURIYA, BABU GUNAGUNI, BABU MITA, DA KAI KARA GA IYAYE KO KAWAYE.

6,  MACEN DA TA DAUKI KANTA LIKITA, MIJINTA MARA LAFIYA, DOMIN YA SAMI KULAWA, TA MUSAMMAN, DA RIRITAWA.

7, MACE MAI SAURIN DAUKAN ISHARA, TANA GANE, SHIRU, DA MAGANA, DA MOTSI, DA YANA YIN SHIGOWA DA FITA, DA SAMU DA RASHI, DA YANA YIN DA AKE CIKI A DUNIYA KO A GARI.

8, MACE MAI SAKAKKIYAR ZUCIYA, MARA KULLI DA RAMUWA,

9, MACE MAI KARAWA MIJI KUZARI, DA KARFIN HALI,  AKAN MANUFAR SA,

10 MACE MAI RIKON AMANAR AURE, DA SOYAYYA GA MIJIN TA KAWAI.

WANNAN MATAR TANA DA WAHALAR SAMU, IDAN KA SAMU IRANTA, KADA KA KUSKURA KU RABU.

YA HALATTA KA AURI MACE FIYE DA DAYA, AMMA KA SANI, MACE DAYA CE KAWAI, TAKE YI MAKA TASIRI A RAYUWA, WACCE RANKA KULLUM YANA KANTA, SAI DAI WACECE WANNAN DAYAR? WANNAN SHINE ABINDA KO WACCE TAKE FATA TA ZAMA, SAI DAI MUYI ADALCI KUMA MU BOYE SABODA GUDUN RIGIMA.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-10 — 10:43 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme