MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: MARTABOBIN MATA GUDA 11 A TARIHIN MUSULUNCI

              Martabobin Mata A Tarihin Musulunci

1-Mace ce Take da darajar samun suna a cikin jerin sunayen Surorin Al-Qur’ani Me Girma. (Babu Sunan Sura Maza sai Mata Suratun NISA’I).

2-Mace Ce Ta fara yin sa’ayi tsakanin safa da marwa (HAJARA A.S).

3-Mace Ce Sanadiyyar Musuluntar Sayyidina Umar R.A (NANA FATIMA A.S)

4-Mace Ce Shari’a ta tanadar mata ladan jam’in salloli guda biyar da Jumu’ah Da Jana’iza Da Jahadi Duk ba sai ta je ba,amma sanadiyyar ta kyautatawa mijinta,Allah zai bata duk ladan wadannan ibadun.

5-Mace Ce Tayi Sanadiyyar Tsiran Sahabbai daga Fushin Allah lokacin da akayi sulhun Hudaibiyya.Kuma MACE CE ta shawo kan sahabbai har suka tsira daga fushin Allah. (UMMU SALAMA R.A).

6-Mace Ce Ta kwantarwa da Manzon Allah (S.A.W) hankali lokacin da Ifk ya faru a Madina,kafin saukar wahayi. (BARIRA).

7-Mace Ce Ta Fara taimakawa Manzon Allah (S.A.W) kuma tana daga cikin Wadanda suka fara karbar Musulunci a duk duniya,kuma ta yiwa addini hidima da dukiyarta da duk abinda ta mallaka har ta bar duniya.Sannan ta haifi shugabar mata (NANA KHADIJA).

8-Mace Ce Sanadin samun taimama a shari’ar musulunci. (UMMUNA A’ISHA).

9-Mace Ce Wadda Manzon Allah (S.A.W) yace idan mutum ya tarbiyyantar da ita koda ba shine ya haifeta ba,zai shiga Aljannah.

10-Mace Ce Ake samun nutsuwa da ita !! Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin LittafinSa., “LIT BARI ASKUNU ILAIHA…”Namiji bazai taba samun sukuni da nutsuwaba sai yana da mata !!!!

11-Mace Ce duk Mulkin Mutum da dukiyarsa sai da ita yake kara kima a idon Mutane !
Kadan Kenan….!!!

MANZON ALLAH (S.A.W) ACIKIN HUDUBARSA TA BANKWANA
Yace: “Ina Yi Muku Wasiya Da Ku Kyautatawa Mata…”.
Allah Ya Bamu Ikon Kyautatawa Mata,Iyayen Al’umma !!

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-09-18 — 11:27 am

1 Comment

Add a Comment
  1. Allah ya kara shiryar mana dasu iyayen duniya. Ah! To ai Sune biyu bisa ukun duniya, sannan kuma sune suka haifi sauran kason. Allah ya yarda da ku iyayenmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme