MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Labarin Wani Bawan Allah Maisuna Yasir Makaho kuma Kurma Sannan Bai Iya Magana Daya Haddace Alqur’ani

                     Miye Hujjarka Na Barin Ibadar Allah-Karanta Kaji

Wannan labarin wani bawan Allah ne maisuna Yasir wanda baya ji baya gani kuma baya iya magana ma’ana shi makaho ne kuma kurma,kuma bai magana sai dai kwatance da hannayen sa.

Annbi Muhammad Sallallahu Alaihin Wasallam yana cewa akwai abubuwa biyu da mutane ke asara alokuta daban daban,sune Lafiya da kuma lokaci, domin aikata aikin alkhairi amma kadan ne daga cikin mune ke amfani da wannan dama da Allah ya bamu

Hasashe ya nuna cewa akwai akalla mutane miliyan arba’in da biyar 45 a duniya da basu gani
Sannan ko kasan cewa akwai sama da mutane miliyan dari uku da hamsin 350 da basu ji kuma basu iya magana.

Hakika Allah gagara misali ne kuma shi mai yadda yaso ne ga bayinsa a kowane lamari na duniya,saboda haka kaida Allah ya baka lafiyayyun idanu yakamata kayi kokarin aikata aikin Alkhairi dasu.

Duk da kasancewar Yasir haka,amma yana da buri,shi dai wannan buri na Yasir shine tayaya zai iya ganin fuskar mahaifiyarsa koda sau daya ne a a rayuwar sa.
Ina masu iya gani da ji da iya magana,sannan suna iya ganin iyayen su sai dai kuma basu daraja su kamar yadda Allah ya fada acikin alqur’ani mai tsarki.

Yasir ya haddace alqur’ani mai girma sannan ba zai iya cewa yasan da labarin wuta ko aljannah ba saboda kasancewar sa ahaka,kwata kwata baida labarin cewa Allah ya turo annabi Muhammad (_S.A.W_),bai san komai akansa bah,sai dai kuma azuciyar sa yasan cewa akwai Allah mamallakin duniyar nan.

Akoda yaushe Yasir baida wani aiki illah bude littafin Allah shafi shafi tunda daga fatiha zuwa baqara a kowane yini tare da motsa bakinsa.

Kai dake da lafiya miye hujjarka ta barin littafin Allah,idan har wanda baya ji baya gani zai iya yini yana duba littafin Allah duk da cewa baya ganin abinda ke rubuce amma Allah ya nuna ayar sa akan wannan bawa nashi ta hanyar bude masa zuciyar sa.

Jama’a musulmi yakamata mu farga mu koma zuwa ga littafin Allah alqur’ani mai tsarki,wannan bawan Allah Yasir yana san yayi magana amma yakasa saboda baida baki,toh kai dake harshe na magana sau nawa kake tuna ni’imar da Allah yayi maka ta harshe da baki,sau nawa kake kadaita Allah dashi sannan sau nawa kake gode masa bisa wannan tarin ni’ima.

Kada ka manta cewa ranar lahira akwai abin awon zunubi da lada.wa’anda ma’auninsu na aikin alkhairi ya rinjayi na sharri sune sukayi nasara,sabanin haka kuma shine babbar asara a duniya, saboda haka kada kabari kyalekyalen duniya ya dulmiyarka da imaninka.

Ga duk wanda Allah bawa lafiya da ji da gani tabbas Allah ya bashi hanyar da zai iya tsira daga sharrin duniya dun inganta rayuwarsa ta lahira,sau nawa mutane suke turo bidiyo ta hanyar sada zumunta musamman facebook,Instagram,youtube domin nishadin abokaina da kawaye amma basu iya bude Qur’ani na minti biyar.

Lokuta da dama idan mutum ya bude facebok ko instagram sabo zaka same shi cikin farinciki,amma ba lallae bane idan ya bude littafin Allah ka same shi da irin wannan farinciki.

Na rantse da Allah duk mutumin da daya ya kauracewa litaffin Allah,amma ya maida facebook,twitter da snapchat littafinsa tabbas yayi asara.

Sannan kada mu manta cewa duk abinda muka gani da ido ko ji ko abinda muka fadi da wanda hannayen mu suka aikta da inda kafafun mu suka taka,tabbas sai Allah ya tambaye mu gobe kiyama,hasali su da kansu zasu bada shaida.

Amma Yasir zai tafi mai cike da farinciki kasancewar bai taba ganin komai ba,sannan bai taba yin magana ba bare yayi zancen wata ko gulmar wani ,haka zalika bai taba jin wani sauti ba da zai iya zama haramun gare sa ba.

Abin al’ajabi da ban mamaki duk da lalurar da Yasir yake fama da ita amma hakan bai hana shi ibadar Allah ba,sau nawa muke ibadar Allah a yini,Allah baya bukatar komai daga gare mu,muke bukatar shi,saboda haka yakamata mu bauta masa domin goben tayi kyau sannan mu tsira daga azabar sa.

Makantar Yasir da rashin jin sa ta sanya mutane da dama kan hanya madaidaciya.

Allah ne masanin sirri da yabar rayuwar Yasir a haka,Yasir bai damu da adadin follower ko friends nawa yake dasu ba,illah kawai tayaya zaiyi ibadar Allah iya tsawon rayuwar sa.

Bugu da kari baida masaniya akan yadda labarin wuta da aljannah suke ba,ya tsaya tsayin daka domin ganin ya bautawa mahaliccinsa kota wane irin yanayi.

Wannan labari na rayuwar Yasir yana nuna muna yadda wasu ke amfani da hannaye da kafafuwan su da bakunan su domin aikata aikin zunubi,hakika Allah baya bacci kuma idan yaso ko niyya zai iya karbar duk wata ni’ima da yayi maka.

Saboda haka ‘yan uwa yakamata muyi taka tsantsan sannan mu tuna cewa Allah yana kallon duk wani motsin mu da kuma aiyukan da muke aikatwa a boye ko a zahiri ko a ina muke,saboda haka mu guji aikata aiyuka munana domin kauraracewa fushin Allah.

Allah Ya Tsare Muna Imanin Mu Daga Aikata Aikin Dana Sani,Ya Kuma Kubatar Damu Daga Shigar Wutar Jahannama…Ameen Summa Ameen.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-10 — 4:46 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme