MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: FA’IDAR SUMBATAR BAKIN MACE-INJI SHEHIN MALAMI TIJJANI YUSUF

                                     Sumbantar mace a baki yana da fa’ida matuka inji wani Shehin Malami-Tijjani Yusuf

Sheikh Guruntum yace miyau na Budurwa yana dada kaifin kwakwalwa

Mai bukatar haddar sa ta zauna da kyau ya yawaita sumbantar iyalin sa

Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda.

Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.

A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.

Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-22 — 2:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme