MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: ABIN TSORON DA BABU MAKAWA DOLE SAI MUN HADU DASHI

Imam Haani’ Radiyallahu Anhu yana cewa: Idan Uthman Bn Affan (RA) ya tsaya kan kabari (na mamaci) ya kanyi Kuka har sai ya ji’ka Gemunsa da hawaye. Sai akace masa, kana ambaton ALJANNAH da WUTA Amma Baka Kuka, amma kana Kuka akan ‘KABARI?

Sai Uthman Bn Affan yace naji Manzon Allah (SAW) yana cewa: Shi ‘KABARI shine na farko a cikin MASAU’KAN LAHIRA, duk wanda ya tsira daga gare shi, Lalle dukkan abunda zai biyo baya zai masa sauki, Amma idan bai tsira daga gare shi ba, abunda zai biyo bayansa yafi tsanani.

Sannan Manzon Allah (SAW) yana cewa: Ban ta’ba ganin Abu Mai tsoro ba, face ‘KABARI yafi shi zama abun tsoro. (Bn Majah, 4567; Tirmiziy, 2308; Sahihul Jamiy, 1684).

Allah Ya Sawwake Mana Wahalhalun Zaman Qabari,Allah Kuma Ya Bamu Ikon Amsa Tambayoyin Da Za’ai Mana A Qabari.

Yusuf Bn Adam Kano

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-09-18 — 11:48 am

2 Comments

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme