MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Ibada Ko Nishadi, Samari Da Yan Mata Wajan Sallar Tahajjud?

A yau dandalinVOA ya waiwayi dabi’ar nan da samari da yan mata ke yi a lokacin da ake gabatar da sallar tahajjud , Mal Abdullahi ya ce wannan dabi’a ce da aka dade ana yi, dan haka lokaci ne da samari da yan mata ke mayar da hankali wajan zance ko free call a maimakon yin ibada da kara kusanci ga ubanji.

Ita kuwa Zainab cewa ta yi wannan rashin tarbiya ne kuma laifin iyaye mata ne na rashin cusa wa ‘ya’yansu muhimmancin ibada mussaman ma a loakcin ramadana.

Shima Abdallah, cewa yayi rashin samun walwala da wasu ‘yan mata ke da shi a gidajensu ke sa da zarar sun sami fita sai su raja’a cikin dabi’un da basu dace ba.

Akan batun ne har ila yau muka sami zantawa da Mal Muktar Umar Sharadda, Limamin masallacin juma’a na rijiyar zaki – ya ce wannan yana daga cikin rudi na shaidan, domin ya hana mutum samun rahamar Allah, sannan ya ja hankalin musulmi da su sani cewar ramadana daya ne a shekara sannan dan Adam bashi da tabbacin cewar zai kai wani ramadana.

KARANTA KAJI YADDA: MIJINA YA DAINA SADUWA DANI – INJI WATA MATA

Daga karshe ya bayyana cewar watan Ramadana wata ne na neman rahamar ubangiji da gabatar da wasu bukatu na dan adam, dan haka ya ja hankalin iyaye da matasa su ji tsoron Allah, su kauce ma aikata abubuwa marasa kyau.

Daga Dandalinvoa

A madadin daukacin ma’aikatan Mujallarmu da wakilan mu na ko ina a fadin Duniya da ma wasu jama’a da ke turo mana labarai domin ganin cigaban fadada ayyukan shafin watsa labarai na Mujallarmu.

Shafin Mujallarmu da dauke da mabiya sama da dubu dari Biyu (200,000) a kowane wata da suke shiga sashen labaran mu domin duba abubuwan da Duniya ke ciki a kowace rana.

mu na kira ga daukacin jama’a da su bamu shawarwari domin ganin lamuran mu sun inganta.

Allah taimake mu baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Mujallarmu.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/mujallarmu

Twitter: https://twitter.com/mujallarmu

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: [email protected]

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-06 — 5:32 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme