MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYAH A MUSULUNCI.

A nan akwai mas’aloli biyar kamar haka: Mas’alar farko: Bayani kan “layyah”, hukuncinta da dalilan shar’anta ta, tare da sharuxanta:

1- Bayani akan layyah: Layyah – a harshen larabci – Shine:bYanka abun layya a lokacin walaha. A shari’ar Musulunci kuma Itace: Abun da ake yankawa na raquma da shanu, awaki da tumaki, don neman kusantar Allah maxaukakin sarki a ranar idi.

2- Hukuncin layyah da kuma dalilan shar’antata: Hukuncinta sunna ne mai qarfi ; saboda faxinsa maxaukakin sarki

“Ma’ana: (Ka yi sallah ga Ubangijinka, ka kuma soke raqumi ga Ubangiji) [Kausar:”

2]. Da kuma saboda hadisin Anas
Ma’ana: (Lallai Annabi (SAW) ya yi layyah da raguna guda biyu masu roxin fari da baqi , madaidaita qaho guda biyu, ya yanka su da hannayensa, yana mai anbaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma xora qafarsa a gefen wuyansu).

3- Sharuxan shar’anta layyah: An sunnata layyah ga bawan da sharruxa dake tafe suka samu a wajensa:

1) Musulunci: Layyah ba tabinganta idan wanda ba musulmi ba ya aikata ta.

2) Balaga da hankali: Duk mutumin da bai kasance baligi mai hankali ba, ba a kallafa masa yin layyah.

3) Samun iko da dama: Wannan ikon na tabbatuwa idan mutum ya mallaki qimar da zai sayi abun layyah da shi, bayan ya mallaki abincinsa da na iyalansa, na tsawon ranar idi, da kuma kwanakin sallah guda uku bayanbyinin idi (ayyamu at- tashriq).

MAS’ALA TA BIYU: Da waxanne dabbobi ake layyah?

Layyah ba ta inganta sai in an yi ta da nau’ukan dabbobi masu zuwa:
1- Raquma.
2- Shanu
3- Awaki da tumaki.

Wannan kuma saboda faxinsabmaxaukakin sarki:
Ma’ana: (Kuma ga kowace al’umma mun sanya ibadar yanka; domin su ambaci sunan Allah akan abinda ya azurta su da shi daga dabbobin ni’imah)

[Hajj: 34]. Su kuma “dabbobin al-an’aam” basa fita daga nauo’i guda uku da sukabgabata. Wani dalilin kuma shine: saboda ba a ruwaito cewa Annabi ko kuma sahabbansa ba, cewa sun yi layyah da wata dabbar da ba su ba (kamar kaza ga misali), in banda waxancan nau’uka na dabbobin ni’imah.

Akuya da tinkiya na isa ga mutum daya da kuma iyalan gidansa; saboda ya zo a cikin hadisin Abu-ayyub cewa:

Ma’ana: (Mutum ya kasance a zamanin manzon Allah ya kan yi layyah dabakuya -ko tinkiya-, wa kansa, da kuma iyalan gidansa, sai su ci, su kuma ciyar).

Ya kuma halatta a yi layyah da ” raqumi ko saniya guda daya ” a madadin mutane guda bakwai; wannan kuma saboda hadisin Jabir ya ce:

Ma’ana: (Mun yi layyah tare da manzon Allah a shekarar sulhun hudaibiyyah,bmutane bakwai ga raqumi xaya , itama saniya daya mutane bakwai).

MAS’ALA TA UKU: Sharuxan da ake
kula da su kan dabbar layyah:

1- Shekaru:
a) Raqumi: An sharxanta ya zama ya kammala shekaru biyar.

b) Shanu: An sharxanta su cika shekaru biyu.

c) Akuya: An sharxanta ta cika shekara xaya .

Wannan kuma duka saboda hadisin Jabir cewa lallai Manzon Allah ya ce:
Ma’ana: (Kada ku yi yankar layyah sai dabbar da ake mata laqabi da “musinnah”, sai dai in kun rasa wannan, sai ku yanka “jaza’ah” daga cikin tumaki).

“Musinnah” daga cikin raquma itace: wanda ta cika shekaru biyar. Daga cikin “shanu” kuma itace: wanda ta cika shekaru biyu. Daga cikin “awaki” kuma: wacce ta cika shekara xaya . Kuma ana kiranta “Saniyyah”.
d) Tinkiya: An sharxanta ta zamo “jaza’ah”; wacce kuma itace: ta ke dabwatanni guda shida; wannan kuma saboda hadisin Uqbah xan Aamir yace a lokacin da Annabi ya banibdabbobin layyah don na raba wa sahabbansa, ya ce:

Ma’ana: (Ni na samu “jaza’ah –tinkiya ‘yar watabshida” ne, Sai Annabi yace: To sai ka yi layyah da ita). Da kuma saboda wani faxin na Uqbah xanvAamir.

Ma’ana: (Mun yi layyahbtare da manzon Allah da “jaza’ah daga cikinbtumaki –wato: ‘yar watanni shida-).

2- Kuvutuwa daga aibuka: An sharxanta ga raquma da shanu, awaki da tumakin da za yi layyah da su;bcewa su kasance sun kuvuta daga aibukan da za su sanya naman dabbobin ya qaranta ; don haka; yankwananniyar dabba ba ta isarwa, haka kuma karyayyiya, da mai ido xaya , da maras lafiya; waxannan kuma saboda hadisin Al- bara’u xan Aazibin -t- daga Annabi ya ce:
Ma’ana: (Dabbobi guda huxu basa isarwa a “layyah”: Dabba mai harari-garke wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse).

Kuma ana ” qiyasi ” ga waxannan aibuka guda huxu, duk wani aibin da ke da irin ma’anarsu; kamar dabbar da haqoranta na gaba suka faxi, da wacce mafi yawan kunnenta ko qahonta ya yanke, da makamancin haka na daga aibuka.

Mas’ala ta huxu: Lokacin yanka abun layyah:
Lokacin yanka layyah na farawa ne daga bayan sallar idi ga mutumin da ya sallace ta, ga mutumin da bai sallace ta ba kuma (saboda uzuri): bayanbfudowar rana na yinin idi da gwargwadon lokacin da za a iya yinbraka’oi guda biyu, da hudubobi biyu; wannan kuma saboda hadisin Al-bara’u
dan Aazib yace: Manzon Allah ya ce:
‘Ma’ana: (Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace da yankan layyah akan tafarki, Amma mutumin da ya yi yanka kuma gabanin ya yi sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta). Lokacin yankan dabbobin na cigaba har zuwa faxuwar ranar yinin qarshe daga cikin kwanakin ” attashriq ” (wato: 13/ ga watan: 12); saboda hadisin Jubair xan Muxim – daga Annabi (r ) yace:

Ma’ana: (Dukkanin ranakun ” tashriq” lokacin yanka ne). Abin da ya fi falala shine a yanka abun laiyan bayan an idar da sallar idi; saboda hadisin Al-bara’u xan Aazib lallai Annabi ( r) yace:

Ma’ana: (Abun da zamu fara yininmu wannan da shi, shine mu yi sallar idi, sa’annan sai mu dawo don mu soke abun layyarmu. Duk wanda ya aikata haka to ya dace da sunnarmu, Duk kuma mutumin da ya yanka abun layyansa gabanin haka to ya sani cewa: nama ne ya gabatar da shi ga iyalansa, ba layya ba).

Mas’ala ta biyar: Yaya ake yi da naman layyah? Kuma meke lazimtar mutumin da zai yi layyah idan goman farkon wata suka shigo:

1- Me ake yi da naman layyah? Lallai an sunnata ga mai layyah ya ci daga layyarsa, ya kuma bada kyauta ga dangi da makwabta da abokai, haka kuma ya yi sadaka ga faqirai , wannan kuma saboda faxinsabmaxaukakin sarki:

Ma’ana: (Sai ku ci daga layyarku, kuma ku ciyar da faqiri mai tsananin talauci) [Hajj: 28]. Kuma mustahabbi ne mutum ya kasa naman layyarsa kashi uku: xaya ga iyalan gidansa, xaya kuma ya ciyar da makwabtansabtalakawa, ya kuma badabkyautan kaso na qarshen ;bwannan kuma saboda hadisinbAbdullahi xan Abbas yana siffanta layyar Annabi (r ), ya ce:

Ma’ana: (Zai ciyar da iyalan gidansa xaya -bisa-uku 1 / 3 , ya ciyar da faqirai makwabtansa xaya -bisa-uku 1 / 3 , kuma ya yibsadaka wa masu roqo da xaya – bisa-uku 1 / 3 ). Yana halatta ya ijiye naman layyah fiye da kwanaki uku; wannan kuma saboda hadisin Buraidah Lallai Annabi yace:

Ma’ana: (Na kasance na hana ku ijiye naman layyah fiye da kwanaki uku, to ku ijiye na tsawon yadda ya yi muku).

2- Abun da ke lazimtar mutumin da yake da niyyar layyah idan kwanaki goman zul-hijjah suka shiga: Idan kwanaki goman zulhijjah suka shiga ya haramta ga mutumin da ya nufi yin layyah ya cire gashin jikinsa, ko wani abu daga faratunsa, i zuwa ya yanka layyansa; wannan kuma saboda hadisin Ummu-
salamah (RA) daga Annabi
Ma’ana: (Idan kwanaki goma suka shiga, a wajen xayanku ya zama akwai abun layyah da zai yi layya da shi to kada ya cire wani gashi, ko ya yanke wani farce). A wata
riwayar kuma cewa ya yi:
Ma’ana: (kada ya tava wani abu daga gashinsa da fatarsa).

([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5553), da Muslim (lamba: 1966).

([2]) Ibnu-majah ya ruwaito shi (lamba: 3147), da At-tirmiziy, ya kuma inganta shi (lamba: 1505), Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 2563).

([3]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1318).

([4]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1963).

([5]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba:5557), da Muslim (lamba:1965) -61, lafazin Muslim ne.

([6]) An-nasa’iy ya ruwaito shi (7/219), Alhafiz Ibnu-hajar yace: Isnadinsa yana da qarfi (Fat-hul bariy, 10/15), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu An- nasa’iy, lamba: 4080).

([7]) Malik a cikin ” muwanxa’a ” ya ruwaito shi (248), da Ahmad (musnad, 4/289), da At-tirmiziy (lamba: 1497), ya kuma ce: hadisi ne hasan sahih, da Abu-dawud (lamba: 2802), da An- nasa’iy (7/244), da Ibnu-majah (lamba: 3144), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahih sunan an-nasa’iy, lamba: 4073).

([8]) Bukhariy ya ruwaito shi (6/ 238), da Muslim (3/ 1553).

([9]) Bukhariy ya ruwaito shi (4/ 82), da Albaihaqiy (9/ 295), da Ibnu-hibban (lamba: 1008), da Ad- daraqudniy (4/284), Alhaisamiy ya ce: Maruwaitan da Ahmad da waninsa suka ruwaito hadisin ta hanyarsu amintattu ne (Majma’uz zawa’id, 3/ 25).

([10]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5560), da Muslim (lamba: 1961).

([11]) Alhafiz Abu-musa ya ruwaito shi a cikin “alwaza’if” ya kuma ce: hadisi ne hasan (Ka duba: Almugniy, 8/632).

([12]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977, 3/1564).

([13]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977).

([14]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977).

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme