MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HUKUNCE HUKUNCE GUDA 15 NA AZUMIN RANAR ARFA

Darasi na Farko-(1)

*1-MINENE AZUMIN ARFA*

Azumin Arfa shine yin Azumi a ranar Tara ga Watan Zil-Hijjah ga wanda bai sami ikon zuwa aikin hajji ba,sai ya azuminci wannan yinin da neman kusanci zuwa ga Allah da raya sunnar Manzon Allah SAW.

*2-MINENE FALALAR AZUMIN RANAR ARFA*

Azumin ranar Arfa yana da falala mai yawa ga kadan daga ciki;

i-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805.

ii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.

iii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;
*(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta………..)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853.

*3-MIYASA AZUMIN RANAR ARFA YAKE KANKARE ZUNUBAN SHEKARA 2 AMMA AZUMIN ASHURA’A YAKE KANKARE SHEKARA DAYA*

ابن القيم رحمه الله؛
Yana cewa:
*”Na farko;Saboda ranar Arfa tana cikin watan mai alfarma kafinta akwai wata mai alfarma kuma a gabanta akwai wata mai alfarma,sabanin ranar Ashura’ah”*.

*”Na biyu:Azumin ranar Arfa ya shafi shari’ar wannan al’ummace kadai sabanin Azumin Ashura’ah wanda shi ya shafa wata al’umma wadda bamu ba,dan Allah sai Allah ya rubanya gafararsa akan ashura’ah”*
@بدائع الفوائد(4-211)

*4-MI YASA AKA KIRA RANAR ARFA DA WANNAN SUNA NA ARFA??*

ابن الجوزي رحمه الله:
Yana cewa;
*”Saboda Mala’ika Jibrilu ya kasance yana nunawa Annabi A.S guraran aiyukan hajji,sai yana fada masa عرفت “*.

*”Na biyu saboda Lokacin da Allah ya sauko da Annabi Adamu da Hawaa’ah sun gane junan sune a daidai wajan da ake tsayuwar arfa”*.
@كشف المشكل (2-156).

Allah ne mafi sani

Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-20 — 7:34 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme