MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

HADARIN ZAMBA DA CIN AMANA A MUSULUNCI-Daga Sheikh Sani Maihula

HARAMCIN BUTULCI DA ZAMBA A MUSULUNCI

Idan Allah ya hada ka da abokin zama, makwabci ne a unguwa ko wurin aiki, ko aboki ko abokin kasuwanci ko miji ko mata ko ‘ya’ya  ko mahaifa, ko wani abu makamancin hakan, kamata yayi idan yayi ma ba daidai ba ka tuna alkhairan sa sai su mantar da kai sharrin sa. Babu wani abokin zama face yanada alkhairi da sharri. Idan aka tafiyar da zafin sharrin sa da sanyin alkhairin sa sai a samu Rayuwa Maidadi.
Babban Butulu shine wanda ya manta alkairan Allah na halittarsa da Allah yayi da bashi rayuwa da addini mai kyau da nunfashi da gani da ji da magana da sauran ni’iomin da basu kirguwa, amma kullun sai fadin sharri yake: akwai zafin rana, ba abinci, ba lafiya, ba ba ba….
Allah yana cewa, ” [Ka ambaci lokacin] da Ubangijin ka yayi sanarwa: idan kuka gode zan kara muku, idan kuka butulce kuma lallai azaba ta mai tsanani ce.”
Allah ya bamu ikon yafewa junan mu da godema ni’iomin sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-10 — 9:42 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme