MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Gwamnatin Jahar Kaduna Ta Tanadi Tsaro Domin Gudanar Da Bikin Maulidin Sheik Ibrahim Inyass

Mun Tanadi Tsaro Yayin Gudanar Da Mauludin Sheik Ibrahim inyasa – Gwamnatin Jahar Kaduna

Daga Auwal M kura

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Tanadi Tsaro Don Gudanar Da Taron Mauludin Sheikh Nyass.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tanadi tsaro don gudanar da taron Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass karo na 32 da za a yi na kasa a Jihar Kaduna a Filin Taro na Murtala Square. Wannan babban taro ne da Al’ummar Musulmi mabiya Darikar Tijjaniyya na kusan ilahirin Afirka za su taru a nan Kaduna don tunawa da ranar haihuwar Sheikh Ibrahim Nyass.
Yanzu haka gwamnatin ta jibge jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan -sanda da sojoji da jami’an KASTELEA da na Kiyaye Hadurra da sauran jami’an Tsaro da za su tabbatar an yi wannan taron lafiya.
Karkashin wannan ne, Gwamnatin Jihar Kaduna ke taya Al’ummar Musulmi mabiya Darikar Tijjaniyya murnar zagayowar wannan muhimmiyar rana. Sannan tana sanar da al’umma cewa gwamanti ta tanadi duk tsaron da ya kamata don ganin an yi wannan gagarumin taron lami lafiya.
A karshe Gwamnatin Jihar Kaduna na rokon al’ummar Jihar da sauran bakin da za su zo wannan taro, da su ba jami’an tsaro hadin-kai, su bi doka da oda don ganin an yi wannan taro an watse lafiya.
Bugu da kari , ana rokon masu zirga zirga ta hanyoyin Murtala Square, da Mobil da kuma Alkali su yi hakuri su yi amfani da wasu hanyoyin zuwa inda suke son zuwa don ganin an rage cinkoson da za a samu a hanyoyin.
Da fatan Allah ya sa a yi taro a tashi lafiya.

Updated: 2018-04-14 — 1:49 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme