MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI FALALAR AZUMIN RAMADAN

Malam Nura surajo

Allah mai girma da daukaka ya ce: “Waccan wata falala ce ta Allah yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma Allah ma’ abucin daukakar falala ne mai girma” (62:4). Yana daga cikin Abin da babu sabani a tsakanin malamai game da shi cewa lalle watan Ramadana wata ne mai alkhairi da albarka wanda Allah ya kebance sa da falala mai yawa. Allah mai girma da buwaya ya saukar da littafinSa a matsayin shiriya ga mutane da waraka ga muminai da hujjoji bayyanannu daga shiriya da kuma rabewa (tsakanin karya da gaskiya). Yana shiryarwa zuwa ga hujja mafi karfi kuma yana bayyana tafarkin shiriya. An saukar da shi ne a daren (Lailatul kadri) daren daraja a cikin watan Ramadana mai alkharai. Allah Madaukakin Sarki Ya tabbatar da wannan a fadarSa: “Watan Ramadana ne wanda Allah Ya saukar da Alkur’ ani a cikin sa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewar (gaskiya daga karya), to, wanda ya halarci watan daga cikin ku sai ya azumce sa” (2:185)

Saukar da Alkur’ani a wannan watan yana nuni ne a kan falalar watan, daure shaidanu da rufe kofofin wuta da bude kofofin aljanna wata falala ce da ta kebanci watan Ramadana. Manzon Allah (S.A.W) Ya ce: “Idan watan Ramadana ya zo ana bude kofofin aljanna kuma ana rufe kofofin wuta kuma ana daure shaidanu, kuma duk wannan aiki ana yin sa ne a farkon daren wata mai alfarma”. Saboda fadarsa Manzon Allah (S.A.W) “Idan farkon daren watan Ramadana ya zo ana daure shaidanu da kangararrun aljannu, kuma ana bude kofofin aljanna, ana rufe kofofin wuta, ba a bude kowace kofa daga cikin ta, kuma ana bude kofofin aljanna ba a rufe kowace kofa a cikin ta, sannan sai wani mai kira ya yi kira cewa: “Ya kai mai neman alkhairi fuskanci aikin alhairi, kuma ya kai mai neman aikata sharri ka takaita (bari), kar ka aikata! kar ka aikata” kuma a kowane dare Allah Madaukakin sarki yana ‘yanta wadansu bayi daga wuta. Haka kuma samun daren “Lailatul kadri” a watan Ramadana wata falala ce wadda wannan watan kadai ke da ita” Allah Mai girma da daukaka Ya ce: “Lallai ne mun saukar da shi (Alkur’ ani) a cikin daren “Lailatul kadri” (daren daraja). To me ya sanar da kai abin da ake cewa (Lailatul kadri)? Mala’iku da ruhi suna sauka a cikin sa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni, aminci ne shi daren har fitar alfijiri” (97:1-5)

Saboda haka za mu takaita wannan bayani a kan abubuwa guda uku domin kwadaitarwa a kan azumi kamar haka: ¬

GAFARTA ZUNUBBAI: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya azumci watan Ramadana yana mai imani da Allah kuma yana mai neman lada, to an gafarta masa ayyukan da ya gabatar na zunubbansa”. Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Salloli biyar da juma’a zuwa wata juma’a da watan Ramadana zuwa Ramadana suna karkare zunubban da ke sakaninsu, matukar an nisanci kaba’ira” (manyan zunubai).

KARBAR ADDU’A DA ‘YANTARWA DAGA WUTA: Ana karbar addu’a ta bayi a watan Ramadana cikin kowane lokaci na watan Ramadana, domin fadarsa (S.A.W) cewa: “Lallai Allah (S.W.T) yana da bayi abin ‘yantawa daga wuta kowane yini da dare na watan Ramadana, kuma kowane Musulmin da ya roki Allah yana da wata addu’ a da idan ya yi ana karba masa”.

MAI AZUMI NA CIKIN MASU GASKIYA DA SHAHIDAI: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce “Ya Manzon Allah shin ko kana ganin idan na shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma na shaida kai Manzon Allah ne, kuma na yi salloli biyar na bada Zakkah kuma na yi azumin watan Ramadana, kuma na yi tsayuwarsa, cikin wane matsayi ni ke? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce “Cikin masu gaskiya da shahidai”

A KASANCE TARE DANI A RUBUTU NA GABA DON CI GABAN WADANNAN BAYANAI INSHA ALLAH. MUNA ADDU’AR ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA SADA MU DA DUKKAN ALHERAN DAKE CIKIN WANNAN WATA MAI ALBARKA.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-19 — 12:52 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme