MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani

Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani.

*__★ Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah a dukkan lamuransa.

*__★ Murna da annashuwa sun tabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun.

__*★ Wadatar zuciya ta tabbata ga mutumin da kullum yake gode wa Allah akan kowacce baiwar da yayi masa komai kankantarta, kuma ba ya kai Qarar Ubangiji awajen halittunsa.

*__★ Cikar buri ya tabbata ga Mutumin da kwadayin gamuwarsa da Allah a Lahira ya hanashi dogon burin Zaman duniya.

*__★ ‘Dandanon zakin imani ya tabbata ga mutumin da ya fifita Son Allah da Manzonsa akan komai na duniya da lahira_ .

*__★Lada mai yawa ya tabbata ga Mutumin da ya ji kalmar gaskiya (kamar irin wannan daga ZAUREN FIQHU) kuma ya isar da ita izuwa zukatan al’umma ba tare da jirkita komai a cikinsa ba.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-12-27 — 12:38 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme