MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BIYAYYA GA IYAYE-KADA KA SAKE KA FIFITA MATARKA AKAN MAHAIFIYARKA.

 

Ya ku bayin Allah! Addinin musulunci ya wajabta mana kyautata ma iyayenmu a matsayin wani dan tukuici ga kokarin da suka yi mana sadda babu wanda zai yi mana in ba su ba. Ba a matsayin biyan hakki ba.

Ya ku bayin Allah! Ba wata da’a ko ibada ko aikin lada

da Allah madaukakin sarki ya ba shi muhimmanci a cikin Alkur’ani –

bayan kadaita Allah – kamar

yadda ya bada muhimmanci ga da’ar iyaye.

ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻭﺍﻋﺒﺪﻭﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ

ﺗﺸﺮﻛﻮﺍ ﺑﻪ ﺷﻴﺌﺎ

ﻭﺑﺎﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﺇﺣﺴﺎﻧﺎ ‏) . ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ 36 :

‘Da’ar iyaye na nufin bayyana son su, da darajanta su, da kiyaye

alfarmarsu, da kauce ma

fushinsu da biyan bukatarsu.

Idan mutum ya yi nazarin

wahalar da iyaye suka sha wajen tashinsa da daure ma kuruciyarsa har zuwa sadda zai yi hankali shi kadai ya isa ya nuna masa girman hakkensu a kan sa. To, ina ga

kuma an duba alhakin uwa

na daukar ciki wata tara

tsakanin lafiya da ciwo, laulayi da haraswa,

da kyamar abinci da raunin jiki da nauyin ciki har zuwa ga nakuda wadda wata ‘yar karamar lahira ce mata suke zuwa a mafi

yawan lokuta!

Annabawa sun kasance masu

tsananin biyayya ga iyayensu:

-ANNABI Isma’il da mahaifinsa

Ibrahim sun

gina ka’aba

ﻓﻠﻤﺎ ﺑﻠﻎ ﻣﻌﻪ ﺍﻟﺴﻌﻲ ..

ﻭﺇﺫ ﻳﺮﻓﻊ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ

-ANNABI Isa (AS):

ﻭﺑﺮﺍ ﺑﻮﺍﻟﺪﺗﻲ ﻭﻟﻢ ﻳﺠﻌﻠﻨﻲ ﺟﺒﺎﺭﺍ

ﺷﻘﻴﺎ

-ANNABI Ibrahim (AS):

ﻳﺎ ﺃﺑﺖ ﺇﻧﻲ ﺃﺧﺎﻑ ﺃﻥ ﻳﻤﺴﻚ ﻋﺬﺍﺏ

ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ …

ﻳﺎ ﺃﺑﺖ … ﻳﺎ ﺃﺑﺖ

-ANNABI Nuhu (AS):

ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﻟﻮﺍﻟﺪﻱ ﻭﻟﻤﻦ ﺩﺧﻞ

ﺑﻴﺘﻲ ﻣﺆﻣﻨﺎ …

Annabi SAWW ya nuna mana

muhimmancin uwaye da da’arsu a cikin hadisai da dama:

1. Yardar Allah tana tare da yardar iyaye: Dabarani

2. Da’ar iyaye na daukaka matsayin mutum a Aljanna:

3. Da’ar iyaye tana gaba da

jihadi in ba ya zama fardu aini ba.-Bukhari.

4. Uwa tana da wani karin fifiko saboda karin wahalarta

wajen ciki da nakuda da shayarwa da reno.

Haka ma a cikin tarihin magabata

akwai labarai masu kayatarwa game da bin wannan umurni na ubangiji na biyayya ga iyaye.

1. Mis’ar bin Kidam (RH) ya

taba kawo ma mahaifiyarsa ruwa bayan ta nemi haka amma ko da ya zo ta yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya waye bai tashe ta ba kuma bai tafiyarsa ba.

2. Muhammad bin Al-

Munkadir ya ce, na kwana ina murza kafar mahaifiyata don ta ji dadin bacci,

kanena kuma ya kwana yana

sallah. Ba zan yi fatar ayi

mana musayar lada ni da shi ba.

3. Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ga wani mutum yana tafiya bayan wani dattijo. Sai ya tambaye shi, wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya ce: “kada ka kira shi da

sunansa, kada ka zauna kafin sa, kuma kada kayi tafiya a gabansa.

Bayan haka ya kai dan uwa

musulmi! Ka sani ba wani

laifi a wurin Allah wanda yake gaggauta kama mai yinsa, ya debe masa albarka, ya barkata masa rayuwa

tun a nan duniya kamar cuta

ma iyaye.

Sai ka ga mutum ya damu da

matarsa, ya kula da ‘ya’yansa amma bai ko san halin da mahaifiyarsa take ciki ba. Wani kuma yana cikin ni’ima da jin

dadin duniya iri-iri amma yana nan birni yana sheke ayarsa, amma mahaifinsa ko

na can kauye yana fama da nikar gero da dawa. Ko ka tarar da ya gina babban gida, yana hawan manyan

ababen hawa amma mahaifiyarsa na cikin rubabben wuri kuma

N100 suna ba ta shawa.

Mu gyara ya ku al’ummar

musulmi.

Ga wasu shawarwari guda

(20), duk mutumin da Allah ya albarkace shi da rayuwa tare da dayan mahaifansa ko dukansu ya kamata

ya rike su:

To ai min afuwa zuwa lokaci na gaba Idan Allah ya yarda, don jin wadannan abubuwa guda 20 da mutum zai yi, da ma wasu shawarwari game da wanda ya riski iyayensa.

Allah muna rokanka da ka qara mana soyayyar Manzo S.A.W da ta iyayenmu a zukatanmu, ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu sau da kafa, ka bamu ikon yi musu biyayya gwargwadon ikonmu. Ameen

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-10-08 — 6:05 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme