MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

AYATUSH SHIFA’I (AYOYIN SAMUN WARAKA)

Wadannan sune ayoyin da ake kira AYATUSH SHIFA’I (Ayoyin Waraka) wadanda kullum Zauren Fiqhu yake bada shawarar cewa Mutane su rika amfani dasu acikin sha’anin Magungunan Musulunci.

Duk wanda yake fama da wata jinya acikin jikinsa zai iya karantasu ya tofa acikin ruwa sannan ya rika sha, da kuma shafawa ajikinsa. In sha Allahu Za’a samu waraka daga Allah.

An nakalto daga wani babban Malami daga cikin Malaman Musulunci wato Shaikh Abul Qasim Al-Qushairiy (rah) cewa dansa yayi rashin lafiya mai tsanani. Yace:

“Na fidda tsammani daga warkewarsa, Kuma al’amarin yayi tsanani gareni. Sai naga Manzon Allah (saww) acikin Barci. Da na gaya masa abinda ke damun yarona sai yace mun “MAI YASA BAKAYI AMFANI DA AYATUSH SHIFA’I BA?”.
Bayan na farka daga barcin, Nayi tunani sosai sai na gano cewar ashe ayoyin suna nan agurare shida ne daga cikin Littafin Allah”. (Ga ayoyin nan ajikin wannan Hoton da kuke gani):

“Da na rubuta masa ajikin Farar takarda, na wanke da ruwa na bashi yasha, sai ya tashi kamar wanda aka kunceshi daga Igiya” (Wato ya warke nan da nan).

Ni kaina (Mai Zauren Fiqhu) da chan ina da wani irin ciwon Ulcer (Olsa) mai tsanani wanda nake fama dashi. Amma ashekarar 2004 nayi amfani da wadannan ayoyin tare da Fatiha da Suratul Ikhlas, kuma Allah ya bani lafiya. Na warke sosai. Har yau ciwon bai sake tashi ba.

Sannan na taba yin amfani dashi ga wani bawan Allah wanda yake fama da chuta mai karya garkuwar jiki (HIV AIDS). Kuma alokacin mun ga saukin abun sosai. domin jikinsa ya fara samun kuzari sosai.

Don haka ina jan hankalin ‘Yan uwa Musulmai cewa kuyi amfani da wadannan ayoyin ku rubuta da abu mai tsaeki akan abu mai tsarki, Sannan ku sha. Ko kuma ku rika tofawa acikin ZAM-ZAM kuna sha.

1. Ayah ta 14 acikin Suratut Taubah.
2. Ayah ta 57 acikin Suratu Yoonus (as).
3. Ayah ta 69 acikin Suratun Nahli.
4. Ayah ta 82 acikin suratul Isra’i.
5. Ayah ta 80 acikin suratush Shu’ara.
6. Ayah ta 44 acikin Suratu Fussilat.

TAMBAYOYIN ADDININ ISALAMA , Daga SunnahNewsNigeria
DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990) 08-10-1437 13-07-2016.
Don Allah duk wanda yake da iko, ya kwafi wannan rubutu ya buga, ya rarraba a Masallatai ko Makarantu domin amfanar da Musulmai. Amma don girman Allah kar wani ya chanza koda harafi guda cikin abinda muka rubuta.

Ga lambar wayar Zauren Fiqhu nan don Qarin bayani.
Allah yasa mu dace

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-26 — 6:45 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme