MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

AMSAR TAMBAYA: YAWAN MOTSAWAR SHA’AWA YAYIN HIRA

Slm malam ya gida ya aiki Allah taimaka akan irin taimakon da kakeyi na yau da kullum, malam sunana IBRAHIM dalibinka na zauren fiqhu facebook nake da tambayoyi guda 2 malam wata yarinya ce muke soyayya da ita kuma tayi nisa yanxu dai angama magana xamuyi aure da ita amma malam duk lokacin da muke waya da ita kawai sai enji zakari na yana tashi maziyi yana fitowa ko kuma idan muna fira da ita gaba da gaba kai takai bana eya jurewa wani lokaci sai na rungumeta ko kuma na ta’bata bayan mun gama kuma zanji gabana da damshi kamar maziyyi,kuma wasu lokutan na kanyi sallah ahaka ba tare da nayi dahara ba.
TO MALAM YAYA SOYAYYARMU TAKE IDAN MUNYI AURE? KUMA MALAM YA MATSAYIN SALLAH TA TAKE? 

AMSA
*******
Kamar yadda tambayar taka ka rabata gida biyu, haka nan amsar da zan baka ita ma ta rabu gida biyu:
1. Wannan motsawar sha’awar ya danganta ne da irin yanayin zancen da kukeyi. Watakil kuna yin zantukan batsa, ko kuma wasu abubuwan da shari’a ta hana. Sannan kuma wannan ta’ba jikinta ko rungumarta da kakeyi, duk abubuwa ne na alfhasha wanda shari’a ta hana. Kuma abubuwa ne wadanda suke tauye ma mutum imaninsa.  Manzon Allah (saww) yace: “WALLAHI A SOKA MA ‘DAYANKU KIBIYAR BAQIN QARFE ACIKIN KANSA SHI YAFI ALKHAIRI DAGA TA’BA (KO KUMA SHAFAR)  MATAR DA BATA HALATTA GARESHI BA”. (Hadisi ne Mash’huri).
Kuma wannan abinda kakeyi yana daga cikin abubuwan da zasu zubar muju da alkhairi  ko albarkar dake cikin auren. Samun iyaye nagartattu yakan zama babban ginshikin  samun zuriya tagari. Amma wannan abinda kukeyi yana nuna cewar babu tsoron Allah  a zukatanku kenan. Domin duk mai tsoron Allah ba zai kusanci Zina ba. Tunda Allah  din yace “KADA KU KUSANCI ZINA, DOMIN ITA (ZINA) ALFASHA CE, KUMA HANYAR TA TA MUNANA”.
2. Ta fuskar hukunci kuma, ya halatta ku auri juna tunda abin bai kai ga yin zina ba..      Sannan kuma shi Maziyyi dukkan Malaman Fiqhu sunyi ittifaqi akan cewa shi NAJASA  NE. Don haka bai halatta kayi sallah dashi ba. Har sai kaje kayi tsarki ka wanke gaba  dayan mazakutarka, Sannan ka wankeshi daga jikin tufafinka. Hukuncinka shine zaka  sake dukkan sallolin da ka tabbatar kayi su da Najasar. WALLAHU A’ALAM.
Anan nake so zan ja hankalin iyaye Maza da M ata cewar bai halatta ku rika barin  ‘Yarku tana kebancewa da samari ba.. Bai halatta ku barta daga ita sai shi ba.. Koda ya riga ya biya sadaki. Irin wannan yana haifar da matsaloli da yawa da kuma lalacewar al’ummah. Allah shi kiyayemu ya kare mana dukkan zuriyarmu daga afkawa cikin
zina da dangoginta. Aaameeen.

Matsalolin Aljanu da Sihiri

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-09-26 — 11:10 am

12 Comments

Add a Comment
 1. Abubakar Abba Toyawa

  Ameen, ALLAH (S.W.T) ya shiryemu.

 2. Abubakar Abba Toyawa

  Ameen, ALLAH (S.W.T) ya shiryemu baki daya.

 3. Masha Allah

 4. amen summa ameeen

 5. muhammad Attahir kmalamai

  Allah ya saka da mafi alkhairin sa

 6. Allah ya kare mu,ya kare zuri’ar mu,dama sauran yan’uwa musulmai baki daya.

 7. mungode mlm

 8. Mungode Allah ya bada lada

 9. Alhussain Muhammad

  Allah ya saka da alheri

 10. Muhammad Lawal Abdallah

  Sannan karin bayani koda kunyi ZINA tare da ita zaka iya auren ta don HARAMUN baya HARAMTA HALAL. Don zina haramun ne shi kuma aure halal don haka zina bata hana aure sai dai da sharadin sai tayi tsarki wato ISTIBIRA’I. Abunda ake nufi da istibira’i shine zata kaurace maka da duk wani namiji har sai tayi tsarki HUDU wasu malamai suka ce tsarki UKU. Daga nan zaka iya auren ta. ALLAH YASA MUDACE AMIN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme