MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BABBAN BURINA A DUNIYA NAGA HADIZA GABON — MATASHI LUKMAN

Babban Burina A Duniya Na Hadu Da Hadiza Gabon — Inji Matashi Lukman

Daga Auwal M Kura

24 /05/2018

K

amar Yadda Hausawa Kance Kowa Da Abunda Ya Dameshi Haka Kuma Kowa Da Masoyinshi, Lallaikam Wannan Batu Haka Yake.

Na Samu Damar Zantawa Da Wani Matashi Dan Asalin Jahar Naija Wanda Yanzu Haka Yana Zaune Garin Kano Tsawon Shekaru Hudu Domin Kawai Allah Ya Hadashi Da Daya Daga Cikin Fittun Jaruman Masna’antar Kannywood, Wato Jaruma Hadiza Aliyu Gabon,

Wakilinmu Auwal M Kura Ya Samu Damar Tattaunawa Da Wannan Matashi Mai Kimanin Shekaru 23 A Duniya Mai Suna Lukuman Wanda Akeyi Masa Take Da (Na Gabon)

Ga Kadan Daga Cikin Yadda Tattaunawa Tasu Ta Kasance:

Auwal M.kura: A Takaice Zanso Sanin Sunanka da Kuma Takai Tattacen Bayani A kanka?

Lukman: Sunana Lukman Amma Amfi Kirana da Na Gabon, Yan Zu Haka Inada Kimanin Shekaru 22 zuwa Da Uku Sannan Ni Haifaffan Garin Naija Ne, Kuma Nazo Jahar Kano Tsawon Shekaru Hudu Ke Nan .
Auwal M.kura: Mai Ya Kawo Jahar Kano?
Lukman : Toh Babban MaKasudin Zuwana Kano Tun 2014 Shine,Nazo ne Domin Na Hadu Da Hadiza Aliyu Gabon,

Auwal M.kura: Toh Tsawon Wannan Shekaru Ko Kasamu Damar Ganin Ita Hadiza Gabon Din ?

Lukman: Gaskiya Aa
Auwal M. Kura: Bakabi Hanyoyin Da Kasan Zaka Ganta Bane ?

Lukman: A Tsawon Wadannan Shekaru Kullum Cikin Bin Duk Wata Hanya Da Zaisa Ko Sau Daya Na Ganta ne , Amma Haryanzu Bamu Hadu Ba,Akwai Gurare Da Yawa Wanda Har Kudi Sukan Amsa A Gurina Da Sunan Zasu Hadani Da Ita Amma Daga Baya Bazasu Hadani Da Ita Ba, Numbobin Waya kam Inada Sama Da Guda Ashirin Wanda Duk Sai Nabiya Ake Bani Ana Cemin Ta Hadiza Gabon Ce Daga Baya Koda Nakira Sai Wani Can Daban Zanji Ya Dauka ,

Auwal M kura: Toh Ganin Yadda Ka Fuskanci Wadanan Kalubale, Kuma Baka Cimma Muradinka Na Ganin Abar Began Taka Ba , Wato Hadiza Gabon, Baisa Kaji Ka Hakura Ba?
Lukman: Kokadan Illa Kara Samun Karfin Gwaiwa Danayi, Domin Kuwa Yanzu Haka Nayi Mata Wakoki Da dama Ko Allah Zaisa Wakar Taje Gareta,

Auwal m.kura: Mai Yasa Duk Sauran Jaruman Hausa Film Nan, Kai Kazabi Hadiza Gabon?
Lukman: Ni Dai Kawai Ita Allah Ya Samun Naji Tana Burgeni , Kuma Ina Matukar Girmamata Saboda Mace Mai Tausayi Da Kamala,

A Karshe Wani Kira Zakayi Da Ita Wannan Jarumar Da Kuma Hanyar Da Zata Sameka Koda Ta Ga Wannan Fira Da Mukayi Da Kai Don Ganin Kun Hadu Da Juna?

Lukman: Toh Ni Yanzu Ina Zaune A Kano ne, Amma Idan Allah Yasa Wannan Sako Ya Isheta , To ina ronkanta Data Cika Burin Na Haduwa Da Ita, Domin Kuwa Burina A Duniya Shine Naga Na Hadu Da Hadiza Aliyu Gabon, Ta Hanyar Tuntbarka Dan Jarida(Auwal M Kura) Ko Gidan Jaridu

Koda Jaruma Hadiza Aliyu Gabon Ta Gamu Da Wannan Sako Zata Iyya Tuntunbar Gidajen Jaridu Kamar Haka:
Jaridar Tarayya
Mikiya
Rariya
Mujallarmu.com
Arewatimes.com.ng

Ko Kuma Matashin Dan Jarida
#Auwal M Kura A Number Kamar Haka : 07033951040

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-24 — 3:37 pm

1 Comment

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme