MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KWANAKI 6 KENAN HAR YANZU BAI TASHI DAGA BARCI BA – YAN SANDA KAN MAIGARKUWA DA MUTANEN DA YA SHA TRAMADOL

Wani mai garkuwa da mutane da har yanzu ba’a san sunansa ba yana hannun hukumar yan sandan jihar Ondo kuma har yanzu yana barci a ofishin hukumar.

 Jami’an yan sandan jihar sun damkeshi ne ranan Lahadi yayinda shi da abokansa uku sukayi kokarin garkuwa da wani mai shago a garin Owo. Game da cewar hukumar yan sanda, matasan sun fasa wani shago ne da bindigogi domin garkuwa da mai shagon amma basu samu nasara ba, sai sukayi kokarin arcewa ta bayan gida.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme