MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

[Ra’ayi] Hanyoyin maganin barayin Gwamnati a Najeriya

Kamal Saidu Dansadau

Babu mai iya hana barayin Gwamnati sata a Najeriya sai Talakawa

Nasan da dama Jama’a zasu iya yadda da wannan furuci nawa idan suka karantan cikakken bayanin nan nawa musamman idan basu saka son zuciya ba.

A najeriya an dade ana cin zarafin talaka, ana yi masa abunda ake so musamman bayan an gama amfani dashi anci zabe. wannan furuci nawa na cewa babu mai iya hana barayin gwamnati sata sai talaka nasa da dama talakawa ba zasu fahimci wannan ba amma kuma nasan kowa zai yadda dani cewa babu yadda zaayi dan siyasa yaci zabe a najeriya sai da hadin kan talaka, koda wajen bashi kudi domin ya jefa kuria, ko wajen magudi. hakan na nufin cewa talaka nada matukar mahimmanci a siyasar najeriya kuma yana nufiin talaka zai iya takawa barayin gwamnati burki akan irin satar da suke.

hanyoyin da zaa iya bi a hana su sata shine:

  1. A ki zaben su koda sun bada kudi
  2. kada mu rika kare barayi musamman idan akwai hujjar cewa sunyi sata
  3. ana iya yun kurin dawo su gida kamar yadda ake yunkurin dawo da Sanata Dino gidan, wajen kai korafi a Hukumar zabe
  4. Sannan kuma adena goyon bayan duk dan siyasar da aka san yana dahannu wajen cin hanci da rashawa musamman wadan muka tabbatar da hukumar EFCC tatabbatar da su barayine koda kotu ta bada belin su.

yin hakan abu ne mai matukar mahimmanci a rayuwar talakawan najeriya dan haka mu tashi tsaye domin magance wannan matsalar.

Updated: 2017-07-02 — 9:25 pm

1 Comment

  1. TALAKAWA KAIDAINE KE IYA HANA BARAYIN GWANNATI SATA

Comments are closed.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme