MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI BURIN SHUGABANNIN NAJERIYA AKAN TALAKAWA DAGA ABDULMALIK SAIDU MAI BIREDI

WANNAN SHI NE HALIN MAFIYA YAWAN SHUWAGABANNINMU!

Abdulmalik Saidu Mai Biredi

Ina ma yadda mu ke sonsu, haka su ke sonmu!
Ina ma yadda mu ke biyarsu da farar aniya haka su ke biyarmu!

Muna son su zama wasu, Amma su kullum gurunsu mu mutu muna yi masu bautar da iyayenmu sunka, rayu suna yi masu!

Kullum gurunsu mu mutu jahillai a kaskance!

Mu kula ‘yan uwa Mafiya yawan ‘yan siyasarmu, suna son mu rabe su ne, Amma lokacin da zabe ya karato, in ya wuce sun hau kan karagar mulki. In mun Kira ba su dauka, in mun matse su, sukan yi muna fuskar shanu!

Mu kula kalilan ne, daga cikinsu ke kaunar mu yi karatu, har suna taimaka muna Dan mu zama wasu.
Amma Mafiya yawansu, lokacin da sunka ga mun kamo hanyar neman ilimi sukanyi duk Mai yuyuwa Dan ganin ba mu Kai ba.

Dan haka sai mu karatun ta natsu Dan ganin mun banbance tsakanin aya da tsakkuwa!

Updated: 2018-01-07 — 9:47 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme