MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

IRIN ABUN KUNYAN DA YA FARU A MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA

A jiya nayi karo da wannan hoton dake  dauke da bayanai akan gayyatar taron da akayi jiya domin karrama Sanata Dino Melaye akan shine Sanata da yasha  gaban kowane Sanata a Najeriya cikin wannan Shekara.

A ganina abun kunyane a Majalisa ace har  IRIN wannan Sanata shi ake karramawa haka. Abun tambaya fa anan  shine:

Shin sauran Sanatocin barci suke ne a Majalisa kokodai an bashi ne da wata manufa?

Shin wai  an manta da cewa jama’ar SA ma na kuka  dashi saboda har  suna kira da INEC ta dawo dashi Gida?

Wai  wane IRIN rawa ne ya taka a Majalisar?

 

A gaskiya a nawa  raayi akwai Sanatoci da dama da suka ri cancanta.

Updated: 2017-10-10 — 6:31 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme