MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: WASU GWAMNONI SUN FARA NEMAN SHAWARAR EL’RUFA’I KAN YADDA ZASU SHIRYA JARABAWAR GWAJI GA MALAMAN MAKARANTA-karanta Kaji

Gwamnonin jihohi zasu shirya jarabawar gwaji ga Malaman Makaranta

Dangane da batun gudanar da sahihin gyara a bangaren ilimi a jihohin kasar nan da ma kasar gabaki daya, wasu gwamnonin Najeriya sun shirya sa kafan wando daya da tabarbarewa Ilimi.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana a shafinsa na sadarwar zamani, Twitter cewa wasu gwamnonin Najeriya sun fara tuntubarsa, don sanin hanyoyi daya dace su bi wajen gudanar da jarabawar gwaji ga Malaman makarantun jihohinsu.

Kwamishinan Ilimin jihar Kogi yana amsan bayanai Dandalin Mujallarmu.com ta ruwaito Gwamnan yana fadin cewa gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da baiwa jihohin da suka nuna sha’awar gudanar da irin wannan jarabawa duk wasu bayanai da suka bukata, tare da basu goyon bayad don ganin an inganta fannin ilimi.

El-rufai ya bayyana haka ne yayin da kwamishinan Ilimi na jihar Kogi, J.S Tolorunleke ya kawo ziyara zuwa Kaduna don samun bayanan yadda aka shirya jarabawar a Kaduna, don su ma su shirya jarabawar a jihar su.

Shugaban mulki na hukumar Ilimi na bai daya, SUBEB, Alhaji Abubakar Salihu ne ya mika ma kwamishinan takardun dake kunshe da bayanai dangane da tsare tsaren jarabawar, inda shi ma kwamishinan ya yaba ma kokarin gwamnatin jihar Kaduna, karkashin Nasir El-Rufai.

 

Updated: 2017-11-13 — 4:14 pm

3 Comments

  1. TO ALLAH GAMU GAREKA,ai indai jarabawa ake bukata ba malamai sukafi chanchan ta ba, (SHUWAGABANNI YAFI A MUSU JARABAWA) don 70% to 80% basusan ya ake shugaban chi ba, kuma wasuma basu kwali mai kyau a harkan ilimin boko, amma bamuce mai SSCE,DIPLOMA KO NCE BAZAI KARA MULKI BA SAI MAI DIGREE. duk da rashin biyan malamai hakkinsu na albashi amma sai annemi tozarta wani. to ALLAH GAMU GAREKA.

  2. sunusi umar sunusi

    allah ya taimake mu

  3. Ba sai ya zubar da su ba. Ya dauki kwararro ya sa a cikinsu. Sannan ai dole hakan ta faru saboda kowa ne bangare kunfi bashi mahimmanci fiye da na malaman furamari. Misali ka doba ko a jikinsu da abun da suke hawa nan za ka fahimta. Idan ka kwatanta da malaman sakandiri ko nagaba da sakandiri. Ai mafiyawan su ba iyawa a busuyi ba, hakinsu ne Allah yan nuna. Domin kafin a dauke su duk an yi masu abunda ya fi wannan gwajin da kayi. In ko haka ne to a koma sama wadan da nayi masu gwaji da gwamnatocin da na daukesu duk ba su san komai ba. Sannan makarantun da sun kayi suma ba su san aiki ba. Kuma kamar yadda za ka bi ka sake daukar wasu. To haka aka yi aka daukesu can da. Haba malan gwamna a canza tunanai a yi nazari.

Comments are closed.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme