MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: MARYAM SANDA TANA DAUKE DA CIKIN MARIGAYI BILYAMINU WATA UKU-Inji Cewar ta-Karanta Kaji

Ina Dauke Da Cikin Tsohon Mijina Marigayi Bilyaminu Wata Uku-Inji Maryam Sanda.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari Maryam Sanda wadda ta kashe mijinta marigayi Bilyaminu har lahira a watan Nuwambar Shekarar data gabata 2017 tana dauke da ciki wata uku inji cewar lauyan ta.

Rahoto dake zuwa muna daga kotun da ake  sauraron shari’ar Maryam Sanda da dangin Marigayi Bilyaminu a jabi Abuja.

Lauya mai kare Maryam Sanda ya tabbatarwa kotu cewa Maryam din tana dauki da cikin marigayi Bilyaminu wata uku,abisa dalilin haka yake son kotu ta bashi belin ta.

Sai dai kuma a bangaren lauyaN dake jagorantar dangin na Bilyaminu yace wannan zancen kangon kurege ne,saboda haka yana son kotu tayi watsa da wannan zance.

Wannan dai shine karo na biyu da lauyan dake baiwa Maryam Sanda karewa ya bukaci kotu data bashi belin maryam tun bayan faruwar al’amarin.

 

KO MIYE RA’AYINKU GAME DA WANNAN ZANCE NA CIKI DA AKACE MARYAM SANDA TANA DAUKE DASHI TSAWON WATA UKU.

 

Updated: 2018-02-06 — 11:23 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme