Labari Da Duminsa: Cutar Lassa Fever Ta Kashe Kwarrun Likitoci Biyu A Jihar Ebonyi.
marubuci:Haruna Sp Dansadau.
Rahoton da muke samu daga Babban asibitin jihar Ebonyi a safiyar yau litinin 15 ga watan janairu.
Cutar zazzabin lassa Fever ta kashe wasu kwararrun likitoci biyu dake aiki Asibitin Abalikiti dake jihar ta Ebonyi.
Har ila yau Dandalin Mujallarmu, ta samu karin bayani daga wasu masu aiki a asibitin, inda suka shaidawa manema labarai sunayen malaman asibitin biyu da suka Mutu.
Ga sunayen kamar haka.
1- Abel Sunday:- Abel Sunday kwararren likita ne a bangaren Ido da hanci (Otorhinolayngology)
2- Dr Ali Felix:- Shima kwararren likita ne daya kwarai fannin magunguna.
Dukkan likitocin biyu sun mutu a bakin aiki sanadiyyar kamuwa da cutar ta lassa Fever daga wasu majinyata dake dauke da ita a asibitin.
Bugu da kari ma’aikatan aibitin sun Nuna rashin jindadin da shiga damuwa bisa wannan babban rashi da sukayi na manya ma’aikata biyu a lokaci daya.
Idan zaka bamu shawara ku turo muna labari akan abinda dake faruwa yankin ku/ki a tuntube mu akan Facebook@mujalarmu ko kuma a WhatsApp 07035169818.
Tunatarwa Kan Cutar Lassa Fever:
Cutar lassa Fever ana gane mai dauke da ita ne idan ya kamu da ita tabbbas.
Alamomi guda 4 ne
1- Mutuwar Jiki, zaiji jikinsa ya mutu sosai.
2- Matsanancin ciwon kai.
3- Amai
4- Yawan jin ciwon gabobi akoda yaushe.
Allah ya kyauta ya kuma muna tsare daga duk wata cuta Ameen.