MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KO MIYE DALILI: KASAR IRAQ TA BAYYANA SUNAN DIYAR SADDAM HUSAINI MAISUNA RAGHAD ACIKIN JERIN SUNAYEN MUTANE 60 DA AKE ZARGIN ‘YAN TA’ADDA NE-Karanta Kaji

Gwamnatin Kasar Iraq Ta Bayyana Sunan Diyar Saddam Husaini Jerin Sunayen Mutane 60 Da Ake Zargin ‘Yan Ta’adda Ne.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Jami’an tsaro na sirri dake kasar Iraq sun tabbatar da sunan diyar marigayi saddam Husaini maisuna Raghad acikin jerin sunayen mutane 60 da kasar Iraq ki ikirarin cewa suna tada zaune tsaye.

Kamar yadda majiyarmu ta¬†Dandalin Mujallarmu,keda labari daga gidan talabijin na kasar Iraq mallakar wani mutum dan kasar Saudi Arabia,bayanai sun tabbatar da cewa sunan ‘yar Saddam Husaini Raghad ya shiga cikin sahun sunayen mutane 60 da gwamnatin kasar Iraq ta lissafa a matsayin ‘yan ta’adda.

Sunan Raghad Husaini ya shiga jerin ‘yan ta’adda ne bisa gudunmuwar da take baiwa ‘yan zanga zanga masu tada zaune tsaye ne a cewar gwamnatin kasar ta Iraq tun a shekarar 2006.

 

Updated: 2018-02-06 — 12:24 pm
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme