MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJ’UN” ALLAH YAYI WA BABBAN LIMAMIN JIHAR LEGAS RASUWA

Duk mai rai mamaci ne: Allah yayi wa babban limamin jihar Legas rasuwa

Babban Limamin Jihar Lagas Ya Rasu – Allah ya gafarta masa, Allah ya baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.
 
Wani labarin jimami da ya same mu ba da dadewa ya nuna cewa Allah ya karbi ran babban limamin jihar Legas mai suna Haruna Akinola.
Babban limamin dai ya rasu ne a jiya lahadi a can garin na Legas.
Labarin da muka samu har ila yau da na nuni cewa ya rasu ne bayan ya sha fama da yar gajeruwar rashin lafiya inda yayi jinya a asibitin koyarwa ta jami’ar jihar Legas.
Dandalin Mujallarmu,ta samu cewa tuni dai akayi jana’izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a jihar ta Legas kuma jana’izar ta samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na jihar da ma kasar baki daya.
Haka ma dai tuni har an fara tururwa zuwa gidan mamacin domin yi ma iyalan sa ta’aziyyar sa.

Updated: 2017-09-25 — 10:16 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme