MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DUBA KAGAHOTUNA: SHUGABA BUHARI YAKAI ZIYARA JIHAR NASARAWA A SAFIYA YAU TALATA-Karanta Kaji

Shugaba Yakai Ziyara Ta Musamman Garin Lafiya Dake Jihar Nasarawa  Saboda Duba Wasu Aiyuka.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shugaban kasa Muhammad Buhari a safiyar yau talata 6 ga watan Fabrairu yayi tattaki na musamman zuwa jihar Nasarawa saboda duba wasu muhimman ayyuka da kuma bude wasu kananan asibitoci a garin Lafia.

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari shugaba Buhari ya ziyarci jihar ta Nasarawa ne bisa duba wasu  ayyukan da gwamnatin tarayya ta dauke nauyin yi a jihar ta Nasarawa a garin lafiya.

Shugaba Buhari ya samu karbuwa sosai musamman daga jama’ar garin lafia,inda dubun masoya maza da mata sukayi farincikin wannan ziyara daya kai masu.

Har ila yau shugaba buhari ya zarce kai tsaye zuwa kananan asibotin da gwamnatin jihar Nasarawa ta bude a karamar hukumar lafia,tare da duba wasu sabbin ayyukan da gwamnatin Nasarawa keyi a jihar tata.

 

Updated: 2018-02-06 — 1:36 pm
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme