MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

BAN TAFI KANO SABODA SIYASA BA SAI ABISA WANI DALILI-Inji Osinbajo-Karanta Kaji

       Tafiyata Kano Banyi Don Siyasa Ba-Inji Osinbajo

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin sa na zuwa kano a ranar asabar 3 ga wannan watan na Fabrairu.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari Osinbajo yace bai ziyarci jihar kano ba ranar asabar saboda siyasa kamar yadda wasu suke zato cewa ya ziyarci wasu kungiyoyin siyasa ne a jihar ta kano.

Osinbajo ya kara da cewa abinda yakai shine kano ba komi bane illar bikin Personal Assistant shi Hafiz Kawu da aka gudanar a ranar asabar a garin kano.

Sai dai kuma mutane da dama sun sa idon akan wannan tafiyar ta mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi,inda wasu ke zaton cewa ya gana da wasu ‘yan siyasa ne acikin sirri.

Mai magana da yawun Osinbajo a kafofin yada labarai Mr Laolu Akande ya tabbatar da cewa Osinabjo yayi tafiyar ne kawai saboda Bikin Personal Assistant din sa Hafiz Kawu da aka gudanar a ranar asabar a kano.

 

Updated: 2018-02-06 — 11:54 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme