MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ANA ZARGIN WANI JANAR DA BARAZANAR KAWAR DA SHUGABA BUHARI-Karanta Kaji

       Janar yayi barazanar kawar da shugaba Buhari

An gurfanar da Birgediya Janar Lym Hassan a gaban kotun rundunar soji – An zargi Jami’in sojan da yin barazana ga shugaba Buhari

Anyi zargin ya yada jita-jitan mutuwar shugaba Buhari Wani rahoton murya na Birgediya Janar Lym Hassan ya billo inda akayi zargin yayi barazanar kawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan wani kwangilar tsaro.

Jaridar Cable ta ruwaito cewa an gurfanar da Hassan wanda ya kasance shugaban kula da kwantar da tarzoma a ma’aikatar tsaro a gaban kotun sojoji a ranar 30 ga watan Oktoba.

Ana tuhumar sa akan zarge-zarge guda biyu: Yada jita-jitan cewa Buhari ya mutu da kuma bukatar cin hancin dala 600,000 daga wani kwangilar tsaro.

Mujallar Naij..com ta rahoto cewa Mista Dayo Apata, kakakin gwamnati kan shari’a, yace an kammala kashi na farko na gurfanar da mayakan Boko Haram, a kotu, inda alkali ya yanke wa wasu hukuncin daurin shekaru 23 a gidan kaso.

Wasunsu kuma an sake su, bisa dalilin cewa bassu da laifi ko yara ne kanana, yayin da wasu suka sami zama a gidan wayarwa da aka gida a yankin.

Updated: 2017-11-13 — 3:47 pm
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme