MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

DANDALIN KANNYWOOD: HARKAR FIM YANZU MUKA FARA, KONA SAKE YIN SABON AURE BAZAN DAINA BA-Inji Jaruma Khadeeja Mustapha

Harkar Fim Yanzu Muka Sake Sabon Zama, Ko Na Sake Aure Zan Cigaba-khadijath Mustapha. 
  
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Khadija Mustapha ta bayyana cewa tana da burin cigaba da harkar fim ko da tayi aure a nan gaba.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da tayi da wata mujallar dake buga labaran masana’antar fina-finan Hausa inda tace tana da burin cigaba da shiryawa tare kuma da daukar nauyin fina-finai koda ta yi aure.

   
Jarumar ta kuma zayyana yadda ta dade tana sha’awar yin fim tun tana yarinya karama kafin daga bisani ta tsunduma cikin fim din gadan-gadan da kanta.

Tun da farkon tattaunawar dai jarumar ta labarta cewa ita shekarun ta 27 a duniya sannan kuma ta taba yin aure har ma ta haifi ‘ya daya kafin auren nata ya mutu.

Haka zalika jarumar ta bayyana fim din ‘Matar Hamza’ a matsayin wanda yafi kwanta mata a rai saboda yadda ta fita daga Kano zuwa Zamfara domin yin sa.

 

Updated: 2018-01-12 — 11:33 am
MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme