MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

FADAKARWA: Kuzo mu gyara sallar mu ta shekaru 50

FADAKARWA: Kuzo mu gyara sallar mu ta shekaru 50

Daga Dokin Karfe

Wata rana Alkali Abu Yusuf yana tafiya da abokansa sai ya ji wani saurayi mai suna Hatin yana magana akan zuhudu (Gudun duniya), sai Alkalin yace wa abokansa mu shiga cikin Masallaci wajen wannan saurayi mu tambaye shi, idan ya amsa mana mu zauna mu saurare shi.

Yayin da suka shiga cikin masallaci sai suke tambaye shi ”Ya kai saurayi bamu labari dangane da Sallah”.

Sai yace musu: ”Shin kuna tambayata ne dangane da ladubbanta ne ko kuma dangane da yadda ake yinta?”.

Sai Alkali Yayi mamaki, mun yi masa tambaya
daya shi kuma ya maida ita tambayoyi biyu, sai yace masa ka bani labari dangane da ladubbanta.

Sai Hatim yace musu ”Ladubbanta su ne; ka tashi da umarnin Allah, ka tafi don neman lada, ka shiga da niyya, kayi kabbara da girmamawa, kayi karatu da tartili (jerantawa), kayi ruku’u da
kushu’i, kayi sujjada da kan kan da kai, kayi tahiya da iklasi (tsarkake niyya) sannan kayi sallama da rahama” Sai Alkali Abu Yusuf Yace:
”ka bani labari dangane da yadda ake yinta!” sai Hatim yace: ”Ka sanya ka’aba a tsakanin goshinka, mizani a tsakanin idanuwanka, siradi a karkashin kafafuwanka, aljannah a hannun damanka, wuta a hannun hagunka, mala’kan mutuwa a bayanka yana nemanka, kuma baka sani ba sallarka za’a karba ne ko kuma za’a maido maka da ita” sai Alkali Yace: ”tun yaushe
kake irin wannan sallar!” sai Hatim Ya amsa masa da cewa:

”Tun shekaru ashirin” sai Alkali Abu Yusuf ya juyo wajen abokansa yace musu: ”Ku zo mu je mu gyara sallarmu ta shekaru hamsin da suka
wuce”

Ya Allah Ka sanya mu daga cikin masu tsayar da Sallah yadda take da dukkan ladubbanta…

Updated: 2018-05-18 — 10:56 am

1 Comment

  1. Abubakar Abba Toyawa

    Ameen summa ameen.

Comments are closed.

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme